Wani uba mai shekaru 20 Ashiru Abubakar, dake kauyen Janbiri a karamar hukumar Birnin-Kudu jihar Jigawa, ya shiga wata cakwakiya bayan ya dankarawa matarsa mai suna Hussaina Yusuf saki uku, bayan nan kuma wata kaunar juna ta sake shigarsu, ga shi babu halin auren juna har sai matar ta auri wani mijin daban wanda ba shi ba sannnan ta fito ne zai iya aurenta kamar yadda shari’ar musulumci ya tanadar.
Sai dai su wadannan ma’auratan sun ci gaba da sheke ayarsu duk da ba a mayar da auren ba a tsakaninsu, inda har wani sabon juna biyu ya shiga tsakanin su, wanda bayyanar cikin ya jefa su cikin rudu da fitintinu daban-daban.
Bayan bayyanar cikin Hussaina ta umurci mijin da ya bata dubu 50 domin zuwa asibiti a zubar mata da cikin ganin ba ta hanyar aure bane suka same shi, gudun kar ya jawo masu abin magana a cikin kauyen nasu, sai dai shi mijin nata Abdullahi ya nuna bai da halin wadannan kudaden.
Hakan ne ya sa cikin kaddara matar ta haihu, inda kanin matar ya sanar da tsohon mijin nata cewa tsohuwar matarsa ta haihu ya mace sai ya shirya.
Kwatsam Abdullahi ya dira gidan da tsohuwar matar tasa take wato me jego, inda ya sake yarinyar ya je daji ya binne ta.
Bayan da mai jegon ta garzaya ofishin yan sanda ta yi kara, jami’an yan sanda suka dukufa bincike, inda aka cafko tsohon mijin nata, nan take ya bayyana cewa ya sace yarinyar ya binne ta a daji domin ya ceci uwar daga kudurin da ita ma ta yi niyyar dauka na halaka jaririyar.
Shima a nasa bayani jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Jigawa, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce abin alfahari bayan da jami’an yan sanda suka tasa keyarsa zuwa inda ya binne jaririyar , aka hako ta aka same ta a raye ba ta mutu ba.
No comments:
Post a Comment